Abin da ba shi yiwuwa Shari'a ta yi domin ta kasa saboda halin ɗan adam, Allah ya yi shi, wato ya ka da zunubi a cikin jiki, da ya aiko da Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, domin kawar da zunubi.
Nufin Ubangiji ne bawansa ya yi girma Kamar dashe wanda yake kafa saiwarsa a ƙeƙasasshiyar ƙasa. Ba shi da wani maƙami ko kyan ganin Da zai sa mu kula da shi. Ba wani abin da zai sa mu so shi, Ba kuwa abin da zai ja mu zuwa gare shi.
Da Musa ya nemi bunsurun hadaya don zunubi sai ya tarar an ƙone shi. Ya kuwa yi fushi da Ele'azara da Itamar, 'ya'yan Haruna, maza, waɗanda suka ragu, ya ce,
Haruna kuma ya miƙa hadayar jama'a. Ya ɗauki bunsuru na yin hadaya don zunubi jama'ar, ya yanka, ya miƙa shi hadaya don zunubi kamar yadda aka yi da na farin.
ya ba Isra'ilawa ka'idodin nan. Sa'ad da kowane mutum a cikinsu zai kawo sadaka ga Ubangiji, sai ya kawo sadakarsa daga cikin garkunansa na shanu, da na tumaki, da na awaki.