Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 27:3 - Littafi Mai Tsarki

3-7 Abin da aka ƙayyade za su biya bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. Masu biya Abin da za su biya Maza masu shekara 20-60 Shekel hamsin Mata masu shekara 20-60 Shekel talatin Maza masu shekara 5-20 Shekel ashirin Mata masu shekara 5-20 Shekel goma sha biyar Maza masu wata guda zuwa shekara 5 Shekel biyar Mata masu wata guda zuwa shekara 5 Shekel uku Tsohon da ya fi shekara 60 Shekel goma sha biyar Tsohuwar da ta fi shekara 60 Shekel goma.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 ga yadda ma’aunin biyan zai kasance, mutum mai shekara tsakanin ashirin da sittin, za a biya azurfa hamsin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 27:3
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Dukan wanda aka lasafta shi cikin ƙidayar kuwa zai biya kuɗi bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. Tilas kowanne ya biya wannan, gama sadaka ce ga Ubangiji.


Sai ka fanshe su suna 'yan wata ɗaya a bakin shekel biyar biyar, bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi.


Sai a kimanta tamanin kowane abu bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi.


Yowash ya ce wa firistoci, “Dukan kuɗin tsarkakan abubuwa da ake kawowa a Haikalin ubangiji, da kuɗin da aka tsara wa kowane mutum, da kuɗin da aka bayar da yardar rai, da ake kawowa a Haikali,


Ka karɓi shekel biyar a kan kowane mutum, bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi.


Idan mutum ya keɓe gidansa ga Ubangiji, sai firist ya kimanta tamanin gidan daidai darajarsa, ko gidan mai tsada ne, ko mai araha ne. Yadda shi firist ya kimanta tamaninsa, haka zai zama.


Zai kuwa kai wa firist rago marar lahani daga garken tumaki don yin hadaya ga Ubangiji saboda laifinsa. Za a kimanta tamanin ragon daidai da tamanin hadaya don laifi.


Idan mutum ya ci amana, ya kuwa yi laifi ba da gangan ba, a kan tsarkakakkun abubuwa na Ubangiji, sai ya kawo rago marar lahani daga garken tumaki ga Ubangiji saboda yin hadaya don laifinsa. Za a kimanta ragon da tamanin kuɗi bisa ga ma'aunin azurfar da ake aiki da shi.


Dukan zinariya da aka yi aikace-aikacen da ita na alfarwa ta sujada sadaka ce talanti ashirin da tara ne da shekel ɗari bakwai da talatin bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ