Amma iyakar abin da mutum ya ba Ubangiji ɗungum daga cikin abubuwan da yake da su, ko mutum ko dabba, ko gonarsa ta gādo, ba za a sayar ko a fansar ba, gama kowane abu da aka keɓe mafi tsarki ne ga Ubangiji.
Ka tafi yanzu, ka fāɗa wa Amalekawa da yaƙi. Ka hallakar da dukan abin da suke da shi. Kada ka rage kome, ka karkashe su dukka, da mata da maza, da yara da jarirai, da takarkarai, da tumaki, da raƙuma, da jakai.”
Sa'an nan annabin ya ce wa sarki, “Ubangiji ya ce, ‘Da yake ka bar mutumin da na ƙaddara ga mutuwa ya kuɓuta daga hannunka, haka ranka zai zama a maimakon nasa, mutanenka kuwa a maimakon mutanensa.’ ”