Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 27:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Idan mutum ya keɓe gidansa ga Ubangiji, sai firist ya kimanta tamanin gidan daidai darajarsa, ko gidan mai tsada ne, ko mai araha ne. Yadda shi firist ya kimanta tamaninsa, haka zai zama.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 “ ‘In mutum ya miƙa gidansa a matsayin wani abu mai tsarki ga Ubangiji, firist zai daidaita dacewar ko mai kyau ne, ko marar kyau. Duk darajar da firist ya kimanta, haka za tă zama.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 27:14
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Iyakar abin da aka keɓe wa Ubangiji a Isra'ila zai zama naka.


Sa'ad da aka mayar da gonar a shekara ta hamsin ta murna, za ta zama tsattsarka ta ubangiji kamar gonar da aka keɓe. Firist ne zai mallaka ta.


Amma idan mutumin yana so ya fansa, sai ya yi ƙarin humushin tamanin da aka kimanta.


Idan shi wanda ya keɓe gida nasa yana so ya fansa, sai ya ƙara kashi ɗaya daga cikin biyar na tamanin da aka kimanta, gidan kuwa zai zama nasa.


Idan ya keɓe gonarsa daga shekara ta hamsin ta murna, ba za a rage kome daga cikin tamanin gonar da aka kimanta ba.


Amma idan ya keɓe ta bayan shekara ta hamsin ta murna, sai firist ya kimanta yawan kuɗin bisa ga yawan shekarun da suka ragu kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo. Sai a rage kuɗin tamanin gonar.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ