Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 27:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Amma idan mutumin yana so ya fansa, sai ya yi ƙarin humushin tamanin da aka kimanta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 In mai shi yana so yă fanshi dabbar, dole yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajarta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 27:13
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Idan shi wanda ya keɓe gonar yana so ya fanshe ta, to, sai ya ƙara kashi ɗaya daga cikin biyar na tamanin kuɗin gonar, gonar kuwa za ta zama tasa.


Idan shi wanda ya keɓe gida nasa yana so ya fansa, sai ya ƙara kashi ɗaya daga cikin biyar na tamanin da aka kimanta, gidan kuwa zai zama nasa.


“Idan kuwa har wani mutum dabam ya ci daga cikin tsarkakakken abin ba da saninsa ba, to, sai ya maido abin ga firist, da ƙarin humushin tamanin abin.


Ba zai musaya shi da wani abu ba, ba zai musaya mai kyau da marar kyau, ko marar kyau da mai kyau ba. Idan kuwa ya musaya dabba da dabba, sai duka biyu, abar da aka musaya, da wadda aka musayar, za su zama tsarkakakku.


Zai kuma biya diyya saboda abu mai tsarki da ya yi laifi a kansa. Zai kuma ƙara humushi a kai, sa'an nan ya ba firist. Firist kuwa zai yi kafara dominsa da ragon hadaya don laifi. Za a kuwa gafarta masa.


Firist ɗin zai kimanta tamanin dabbar daidai darajarta, kamar yadda firist ya kimanta, haka zai zama.


Idan mutum ya keɓe gidansa ga Ubangiji, sai firist ya kimanta tamanin gidan daidai darajarsa, ko gidan mai tsada ne, ko mai araha ne. Yadda shi firist ya kimanta tamaninsa, haka zai zama.


Idan dabbar marar tsarki ce, sai mai ita ya kimanta tamanin kuɗinta, ya ƙara da humushin kuɗin, ya saya. Idan ba a fansa ba, sai a sayar bisa ga tamaninta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ