Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 26:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Mutum biyar ɗinku za su runtumi mutum ɗari, mutum ɗari ɗinku za su runtumi mutum dubu goma. Maƙiyanku kuwa za su fāɗi a gabanku ta kaifin takobi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Mutanenku biyar za su kori mutum ɗari, mutanenku ɗari kuma za su kori mutane dubu goma, abokan gābanku kuma za su fāɗi a kaifin takobi a gabanku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 26:8
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Mutuminku guda zai runtumi mutum dubu nasu, tun da yake Ubangiji Allahnku ne yake yaƙi dominku, kamar yadda ya alkawarta muku.


“Ubangiji zai sa ku fatattaki abokan gābanku a gabanku waɗanda suke tasar muku. Ta hanya guda za su auka muku, amma ta hanyoyi bakwai za su gudu daga gabanku.


Ƙaƙa mutum ɗaya zai runtumi dubu, Mutum biyu kuma su kori zambar goma, Sai dai Dutsensu ya sayar da su, Ubangiji kuma ya bashe su?


Abishai ɗan'uwan Yowab kuwa shi ne shugaban jarumawa talatin ɗin. Ya girgiza mashinsa, ya kashe mutum ɗari uku. Ya yi suna a cikin jarumawan nan talatin.


Sai dai kada ku tayar wa Ubangiji, kada kuwa ku ji tsoron mutanen ƙasar. Za mu ci su ba wuya, Ubangiji kuma zai lalatar da gumakansu da suke kāre su. Ubangiji kuwa yana tare da mu, kada ku ji tsoronsu.”


Wannan shi ne labarin manyan jarumawan Dawuda. Yashobeyam ɗan Bahakmone shi ne shugaban jarumawa talatin. Ya karkashe mutum ɗari uku da māshinsa baki ɗaya.


Za ku runtumi maƙiyanku, za su kuwa fāɗi ta kaifin takobi a gabanku.


Ya kuwa sami sabon muƙamuƙin jaki, ya ɗauka ya kashe mutum dubu da muƙamuƙin.


Yahudawan da suke cikin lardunan sarki kuma suka taru, suka kare rayukansu, suka ƙwaci kansu daga maƙiyansu. Suka kashe mutum dubu saba'in da dubu biyar (75,000) daga cikin maƙiyansu, amma ba su washe dukiyarsu ba.


A ranar, Ubangiji zai kiyaye mazaunan Urushalima, har wanda yake marar ƙarfi a cikinsu zai zama mai ƙarfi kamar Dawuda. Jama'ar Dawuda za ta zama kamar Allah, kamar mala'ikan Ubangiji a gabansu.


Sai ku aiki mutum dubu ɗaya daga kowace kabilar Isra'ila zuwa wurin yaƙi.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ