Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 26:4 - Littafi Mai Tsarki

4 sa'an nan zan ba da ruwan sama a lokacinsa, ƙasar kuwa za ta ba da albarkarta, itatuwan gonaki kuma za su ba da 'ya'yansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 zan aika da ruwan sama a lokacinsa, ƙasa kuma za tă ba da hatsi, itatuwa kuma za su haihu ’ya’yansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 26:4
31 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gama za a yi shuka da salama. Kurangar inabi za ta yi 'ya'ya, ƙasa kuma za ta ba da amfani, za a yi isasshen ruwan sama. Ni kuwa zan sa sauran jama'an nan su ci moriyar abubuwan nan duka.


Ƙasa ta ba da amfaninta, Allah, wanda yake Allahnmu ne, ya sa mana albarka.


Zan sa 'ya'yan itatuwa da amfanin gona su yalwata, don kada ku ƙara shan kunya saboda yunwa a wurin al'ummai.


Duk lokacin da kuka shuka amfanin gonakinku, Ubangiji zai aiko da ruwan sama ya sa su girma, zai ba ku kaka mai albarka, shanunku kuma za su sami makiyaya wadatacciya.


Yakan aiko da ruwan sama, Ya shayar da gonaki.


Ubangiji zai buɗe muku taskarsa ta sammai, don ya ba ƙasarku ruwa a kan kari, zai kuma sa albarka a kan dukan aikin hannuwanku. Al'ummai da yawa za su karɓi rance a wurinku, amma ku, ba za ku karɓi rance ba.


zai shayar da ƙasarku da ruwa a kan kari, da ruwan bazara da na kaka. Za ku tattara sabon hatsinku da sabon ruwan inabinku, da manku.


ku sani zan sa muku albarka a shekara ta shida don ta ba da isasshen amfanin da zai kai ku shekara uku.


Duk da haka kuwa bai taɓa barin kansa, ba shaida ba, domin yana yin alheri, shi da yake yi muku ruwan sama, da damuna mai albarka, yana ƙosar da ku da abinci, yana kuma faranta muku rai.”


domin ku zama 'ya'yan Ubanku wanda yake cikin Sama. Domin yakan sa rana tasa ta fito kan mugaye da kuma nagargaru, ya kuma sako ruwan sama ga masu adalci da marasa adalci.


Ubangiji zai arzuta mu, Ƙasarmu kuwa za ta ba da amfanin gona mai yawa.


Ka sa aka yi ruwan sama mai yawa, ya Allah, Ka rayar da ƙasarka wadda ta zozaye.


Suna da ikon hana ruwan sama, don kada a yi ruwa a duk kwanakin da suke yin annabci, suna kuma da iko a kan ruwa, su mai da shi jini, su kuma ɗora wa duniya kowane irin bala'i, a duk lokacin da suke so.


Domin haka, sai ku yi haƙuri, 'yan'uwana, har ya zuwa ranar komowar Ubangiji. Ga shi, manomi yana sa rai ga samun amfanin gona mai albarka, yana kuwa haƙuri da samunsa, har a yi ruwan shuka da na kaka.


A cikin gumakan al'ummai akwai mai iya sa a yi ruwa? Sammai kuma su yi yayyafi? Ashe, ba kai ne ba, ya Ubangiji Allahnmu? Domin haka a gare ka muke sa zuciya, Gama kai ne mai yin waɗannan abubuwa duka.”


Zan bar ciyayi su rufe ta. Ba zan yi wa kurangar inabin aski ba, ko in yi mata noma, amma zan bar sarƙaƙƙiya da ƙayayuwa su rufe ta. Har ma zan sa gizagizai su hana ta ruwan sama.”


Daga sararin sama kakan aiko da ruwa bisa duwatsu, Ƙasa kuwa takan cika da albarkunka.


Wani annabi mai suna Iliya, mutumin Tishbi a Gileyad, ya ce wa sarki Ahab, “Na rantse da Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda nake bauta wa, ba za a yi raɓa ko ruwan sama cikin shekarun nan ba, sai da faɗata.”


Ƙasar za ta ba da amfani, za ku ci, ku ƙoshi, ku zauna lafiya.


“Idan kun yi biyayya da umarnansa waɗanda ya umarce ku da su yau, kun ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kun bauta masa da zuciya ɗaya da dukan ranku,


Allah ya sa mana albarka, Da ma dukan jama'a ko'ina su girmama shi.


Adalci zai yi tafiya a gaban Ubangiji, Yă shirya masa tafarki.


Kada ku ji tsoro, ku dabbobin saura, Gama wuraren kiwo a jeji sun yi kore shar. Itatuwa suna ta yin 'ya'ya, Itacen ɓaure da kurangar inabi suna ta yin 'ya'ya sosai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ