Firistoci 26:30 - Littafi Mai Tsarki30 Zan lalatar da masujadanku, in rurrushe bagaden ƙona turarenku, in jefar da gawawwakinku a kan gumakanku, raina kuwa zai ji ƙyamarku. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202030 Zan rurrushe dukan masujadanku, in yanke bagadanku na turare, in yi tarin gawawwakinku a kan gumakanku, zan kuma yi ƙyamarku. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'ad da aka gama duka, sai dukan Isra'ilawa da suka hallara, suka bi cikin biranen Yahuza, suka farfashe al'amudan, suka ragargaza Ashtarot, suka farfashe masujadai da bagadai duka da suke a Yahuza da Biliyaminu, da na Ifraimu da Manassa har suka hallakar da su duka. Sa'an nan dukan jama'ar Isra'ila suka koma garuruwansu, ko wanne zuwa mahallinsa.
Ya fitar da dukan firistoci daga cikin garuruwan Yahuza, sa'an nan ya lalatar da matsafai na kan tuddai inda firistoci suka ƙona turare, tun daga Geba har zuwa Biyer-sheba. Ya kuma rurrushe matsafai na kan tuddai waɗanda suke a ƙofofin shiga ƙofar Joshuwa, hakimin birnin, waɗanda suke hagu da ƙofar birnin.