Wato alkawarin da na yi da kakanninku a lokacin da na fito da su daga ƙasar Masar, daga cikin tanderun ƙarfe. Na faɗa musu su yi biyayya da maganata, su aikata dukan abin da na umarce su. Ta haka za su zama mutanena, ni kuma in zama Allahnsu.
Gama za a yi shuka da salama. Kurangar inabi za ta yi 'ya'ya, ƙasa kuma za ta ba da amfani, za a yi isasshen ruwan sama. Ni kuwa zan sa sauran jama'an nan su ci moriyar abubuwan nan duka.
Ku kawo dukkan zaka a ɗakin ajiyata domin abinci ya samu a cikin Haikalina. Ku gwada ni, za ku gani, zan buɗe taskokin sama in zubo muku da albarka mai yawan gaske.
Amma idan kun juyo wurina, kun kiyaye umarnaina, kun aikata su, ko da yake an warsatsar da ku can nesa, zan tattaro ku, in kawo ku wurin da na zaɓa domin in sa sunana ya kahu a wurin.’
Duk lokacin da kuka shuka amfanin gonakinku, Ubangiji zai aiko da ruwan sama ya sa su girma, zai ba ku kaka mai albarka, shanunku kuma za su sami makiyaya wadatacciya.