Ubangiji ya aikata abin da ya yi niyya, Ya cika maganarsa wadda ya faɗa tun dā, Ya hallakar, ba tausayi, Ya sa maƙiyi ya yi murna a kanki, Ya ƙarfafa ƙarfin maƙiyanki.
Amma idan ba ku kasa kunne gare ni ba, ba ku kuwa kiyaye ranar Asabar da tsarki ba, kun kuma ɗauki kaya kun shiga ta ƙofofin Urushalima a ranar Asabar, sai in cinna wa ƙofofin Urushalima wuta. Za ta kuwa cinye fādodin Urushalima, ba kuwa za ta kasu ba.’ ”
Ku kula fa, kada ku ƙi mai maganar nan. Domin in waɗanda suka ƙi jin mai yi musu gargaɗi a duniya ba su tsira ba, to, ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi jin wannan da yake yi mana gargaɗi ma daga Sama?
Idan ba za ku kasa kunne ba, idan ba za ku sa a zuciyarku ku girmama sunana ba, to, zan aukar muku da la'ana, zan la'antar da albarkunku. Koyanzu ma na riga na la'antar da su domin ba ku riƙe umarnina a zuciyarku ba, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
Amma kamar yadda Ubangiji Allahnku ya cika alkawaran da ya yi muku, haka nan kuma Ubangiji zai aukar muku da masifu, har ya hallaka ku daga ƙasan nan mai albarka da Ubangiji Allahnku ya ba ku.
Amma duk da haka ba su yi biyayya ba, ba su kuma kasa kunne ba. Kowa ya bi tattaurar zuciyarsa mai mugunta. Domin haka na kawo musu dukan maganar alkawarin nan wanda na umarce su su yi, amma ba su yi ba.”
Kamar yadda aka rubuta a dokokin Musa, haka wannan bala'i ya auko a kanmu, duk da haka ba mu nemi jinƙan Ubangiji Allahnmu ba, ba mu daina aikata muguntarmu ba, ba mu lizimci gaskiyarka ba.
Lokacin da suke tafiya, zan shimfiɗa musu ragata, Zan saukar da su ƙasa kamar yadda akan yi wa tsuntsun da yake tashi sama. Zan hukunta su saboda mugayen ayyukansu.
“Ku tafi ku yi tambaya ga Ubangiji saboda ni, da jama'a, da dukan mutanen Yahuza a kan maganar littafin nan da aka samo, gama Ubangiji ya yi fushi da muƙwarai saboda kakanninmu domin ba su bi maganar littafin nan ba, har da za su yi dukan abin da aka rubuta mana.”
‘Ni Ubangiji, na ce zan kawo masifa a kan wannan wuri da a kan mazaunan wurin, wato dukan la'anar da aka rubuta a littafin da aka karanta a gaban Sarkin Yahuza.
Amma sa'ad da suka shiga cikinta suka mallake ta, ba su yi biyayya da muryarka ba, ba su kiyaye dokokinka ba, ba su aikata dukan abin da ka umarce su ba, saboda haka ka sa wannan masifa ta auko musu.