A rana ta fari ga wata na biyu a shekara ta biyu bayan da Isra'ilawa suka bar Masar, Ubangiji ya yi magana da Musa a cikin alfarwa ta sujada a jejin Sinai. Ya ce,
Sai Musa ya yi magana da Isra'ilawa, suka kuwa fito masa da mutumin da ya yi saɓon a bayan zangon. Suka jajjefe shi da duwatsu. Haka Isra'ilawa suka aikata yadda Ubangiji ya umarci Musa.
“Idan kuma mutanen ƙasar sun kawo kayayyaki da hatsi don sayarwa a ranar Asabar, ba za mu saya ba, ko kuma a wata tsattsarkar rana. “A kowace shekara ta bakwai ba za mu girbe amfanin gonakinmu ba, za mu kuma yafe kowane irin bashi.