Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 24:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Sai a sa lubban tsantsa a kowane jeri don a haɗa da abincin da za a ƙone domin hadaya ta tunawa ga Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Za a zuba turare a kowane layin dunƙulen burodin don yă kasance abin tunawa a bisa burodin. Turaren zai ƙone a madadin burodin don yă zama kamar hadayar da aka miƙa da wuta ga Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 24:7
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zai kuma kawo hadayarsa a wurin 'ya'yan Haruna maza, firistoci. Zai ɗibi tāfi guda na lallausan garin da aka zuba wa mai da dukan lubban. Firist kuwa zai ƙona wannan a kan bagaden don tunawa, gama hadaya ta ƙonawa ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.


Saboda haka, yana da ikon ceton masu kusatowa ga Allah ta wurinsa, matuƙar ceto, tun da yake kullum a raye yake saboda yi musu addu'a.


domin mu yabi ɗaukakar alherinsa wanda ya ba mu kyauta hannu sake saboda Ƙaunataccensa.


ya ce, ‘Ya Karniliyas, an amsa addu'arka sadakarka kuma ta zama abar tunawa ga Allah.


Shi kuwa ya zura masa ido a tsorace, ya ce, “Ya Ubangiji, mene ne?” Mala'ikan kuma ya ce masa, “Addu'arka da sadakarka sun kai har a gaban Allah, abubuwan tunawa ne kuma a gare shi.


Ni ne Gurasan rai da ya sauko daga Sama. Kowa ya ci Gurasan nan, zai rayu har abada. Har ma gurasar da zan bayar naman jikina ne, domin duniya ta rayu.”


Yesu ya ce musu, “Ni ne gurasa mai ba da rai. Wanda ya zo gare ni ba zai ji yunwa ba har abada, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada.


Ubangiji ya ce wa Musa, “Rubuta wannan a littafi domin a tuna da shi, ka kuma faɗa wa Joshuwa zan shafe Amalekawa ɗungum.”


Zai zama matuni kamar alama a hannunku, da abin tunawa a goshinku, domin shari'ar Ubangiji ta zama a bakinku, gama da hannu mai ƙarfi Ubangiji ya fisshe ku daga Masar.


Ranan nan za ta zama ranar tunawa a gare ku, za ku kiyaye ta, ranar idi ga Ubangiji. Dukan zamananku za ku kiyaye ta, idi ga Ubangiji har abada.


Sa'ad da bakan yake cikin girgije zan dube shi, in tuna da madawwamin alkawari tsakanin Allah da kowane mai rai da dukan talikan da suke bisa duniya.”


A sa duwatsun a kafaɗun falmaran domin a riƙa tunawa da 'ya'yan Isra'ila. Haruna zai rataya sunayensu a kafaɗunsa a gaban Ubangiji domin a tuna da su.


Firist zai ɗauki kashi na tunawa daga hadaya ta garin, ya ƙona shi bisa bagaden, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.


Ba ku kawo mini hadayun ƙonawa na tumaki ba, Ba ni kuke girmamawa da hadayunku ba. Ban nawaita muku da neman hadayu ba, Ko in gajiyar da ku da roƙon turare.


A sa'ad da mutum ya kawo hadaya ta gari ga Ubangiji, sai ya kawo gari mai laushi, ya zuba masa mai da lubban.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ