18 Wanda ya kashe dabba kuma ya yi ramuwa, rai maimakon rai.
18 Duk wanda ya kashe dabbar wani, dole yă biya, rai domin rai.
Wanda ya kashe dabba ya yi ramuwa, wanda kuwa ya kashe mutum sai a kashe shi.
sa'ad da mutum ya yi laifi, ya kuwa tabbata mai laifi ne, sai ya mayar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta,
“Idan mutum ya yi wa wani rauni, kowane irin rauni ne ya yi masa, shi kuma haka za a yi masa.
“Idan mutum ya bar rami a buɗe, ko ya haƙa rami bai rufe ba, in sa ko jaki ya fāɗa ciki,