9 Ubangiji ya yi magana da Musa, cewa,
9 Ubangiji ya ce wa Musa,
A kwana bakwai ɗin za su riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa kowace rana ga Ubangiji. Za su kuma yi muhimmin taro a rana ta bakwai ɗin. Ba za su yi aiki mai wuya ba.
lokacin da suka shiga ƙasar da Ubangiji yake ba su, sai su kawo wa firist dami na fari na amfanin gonakinsu.
Ku kuma yi idin nunan fari na amfanin gonakinku da kaka. Sa'an nan kuma za ku yi idin gama tattara amfanin gonakinku a ƙarshen shekara.