A kwana bakwai ɗin za su riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa kowace rana ga Ubangiji. Za su kuma yi muhimmin taro a rana ta bakwai ɗin. Ba za su yi aiki mai wuya ba.
A kan rana ta fari za ku yi tsattsarkan taro, haka kuma za ku yi a rana ta bakwai. A cikin waɗannan ranaku ba za a yi kowane aiki ba, sai na abin da kowa zai ci.
A rana ta goma sha biyar ga watan bakwai za a yi tsattsarkan taro domin yin sujada, ba za a yi aiki ba. Su kiyaye idin da girmama Ubangiji har kwana bakwai.