Ni kaina zan yi gāba da wannan mutum, in raba shi da jama'arsa domin ya ba Molek ɗaya daga cikin 'ya'yansa, gama ya ƙazantar da alfarwa ta sujada, ya ƙasƙantar da sunana mai tsarki.
Taku ta ƙare, ku mazaunan gaɓar teku, ke al'ummar Keretiyawa! Ya Kan'ana, ƙasar Filistiyawa, Maganar Ubangiji tana gāba da ke, Za a hallaka ki har ba wanda zai ragu.
“ ‘Idan aka ruɗi annabin har ya yi magana, ni Ubangiji, ni ne na rinjaye shi, zan miƙa hannuna gāba da shi, zan hallaka shi daga cikin mutanena, Isra'ila.