28 Ba za ku yanka uwar dabbar tare da ɗanta rana ɗaya ba, ko uwar saniya ce, ko ta tunkiya ce.
28 Kada a yanka saniya, ko tunkiya da ɗanta rana ɗaya.
“Kada ku ci mushe. Amma mai yiwuwa ne ku ba baren da yake zaune a garuruwanku, ko kuma ku sayar wa baƙo. Gama ku jama'a ce keɓaɓɓiya ga Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya a madarar uwarsa.”
“Sai ku kawo nunan farin amfanin gonarku a cikin gidan Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya da madarar uwarsa.”
“Wajibi ne ku kawo mafi kyau daga cikin nunan fari na amfanin gonakinku a gidan Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya cikin madarar uwarsa.”