Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 22:27 - Littafi Mai Tsarki

27 “Sa'ad da kuma aka haifi ɗan maraƙi, ko ɗan rago, ko ɗan akuya, zai yi kwana bakwai tare da uwarsa. A rana ta takwas zuwa gaba, sai a karɓe shi don yin hadaya ta ƙonewa ga Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 “Sa’ad da aka haifi ɗan maraƙi, tunkiya, ko akuya, sai yă kasance da mahaifiyarsa kwana bakwai. Daga rana ta takwas zuwa gaba, zai zama yardajje hadaya, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 22:27
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Haka kuma za ku yi da 'ya'yan farin shanunku, da na awakinku, da na tumakinku. Ɗan farin zai yi kwana bakwai tare da uwar, amma a rana ta takwas za ku ba ni shi.


“Ba kuma za ku karɓi irin dabbobin nan daga hannun baƙo don ku miƙa su hadaya ga Ubangiji ba, marasa tsarki ne tun da yake suna da lahani, ba za a karɓa ba.”


Haruna kuwa zai sa shi bisa goshinsa, ta haka zai ɗauki kurakuran da ya yiwu Isra'ilawa sun yi cikin miƙa sadakokinsu masu tsarki. Kullum Haruna zai riƙa sa shi bisa goshinsa don su zama karɓaɓɓu ga Ubangiji.


Sama'ila ya kama ɗan rago ya miƙa shi ɗungum hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ya kuma yi roƙo ga Ubangiji ya taimaki Isra'ilawa, Ubangiji kuwa ya amsa addu'arsa.


“Kada ku yi jinkirin fitar da zakar amfanin gonarku ta hatsi da ta abin matsewa. “'Ya'yan farinku, maza, kuma za ku ba ni su.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ