Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 22:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Dabbar ta kasance namiji marar lahani idan ana so ta karɓu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 dole ku miƙa dabba namiji marar lahani, daga shanu, tumaki, ko awaki, domin yă zama yardajje a madadinku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 22:19
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Idan hadayarsa ta ƙonawa daga cikin garken tumaki ko kuwa na awaki ne, sai ya ba da namiji marar lahani.


Idan sadakarsa ta hadayar ƙonawa ce daga cikin garken shanu, sai ya ba da namiji marar lahani, zai miƙa shi a ƙofar alfarwa ta sujada domin sadakar ta zama abar karɓa a gaban Ubangiji.


Domin Almasihu ma ya mutu sau ɗaya tak ba ƙari, domin kawar da zunubanmu, mai adalci saboda marasa adalci, domin ya kai mu ga Allah. An kashe shi a jiki, amma an rayar da shi a ruhu.


sai dai da jinin nan mai daraja na Almasihu, kamar na ɗan rago marar naƙasa, marar tabo.


domin shi kansa yă ba kansa Ikkilisiya da ɗaukakarta, ba tare da tabo ko tamoji ba, ko wani irin abu haka, tă dai zamo tsattsarka marar aibu.


Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi zunubi saboda mu, domin mu mu sami adalcin Allah ta wurinsa.


Sai Bilatus ya sāke fitowa, ya ce wa Yahudawa, “Ga shi, zan fito muku da shi, domin ku san ban same shi da wani laifi ba.”


Sa'ad da jarumin ya ga abin da ya gudana, sai ya girmama Allah ya ce, “Hakika mutumin nan marar laifi ne!”


Mu kam, daidai aka yi mana, don hakika sakamakon aikinmu muka samu, amma mutumin nan bai yi wani laifi ba.”


ya ce masu, “Kun kawo mini mutumin nan a kan, wai yana ɓad da jama'a, na kuwa tuhunce shi a gabanku, amma ban same shi da wani laifi a ƙararrakinsa da kuka kawo ba.


Sa'ad da jarumin da waɗanda suke tare da shi suna tsaron Yesu suka ga rawar ƙasa da kuma abin da ya auku, sai duk tsoro ya kama su, suka ce, “Hakika wannan Ɗan Allah ne!”


Da Bilatus ya ga bai rinjaye su ba, sai dai hargitsi yana shirin tashi, sai ya ɗibi ruwa ya wanke hannunsa a gaban jama'a, ya ce, “Ni kam, na kuɓuta daga alhakin jinin mai adalcin nan. Wannan ruwanku ne.”


Banda haka kuma, a lokacin da yake zaune a kan gadon shari'a, sai mata tasa ta aiko masa da cewa, “Ka fita daga sha'anin mara laifin nan, don yau na sha wahala ƙwarai a mafarkinsa.”


ya ce, “Na yi zunubi da na ba da marar laifi a kashe shi.” Suka ce, “Ina ruwanmu? Kai ka jiyo!”


Idan kuwa daga cikin 'yan tumaki zai ba da hadayarsa, sai ya kawo 'yar tunkiya marar lahani.


Tilas ne dabbar ta kasance lafiyayyiya ƙalau, bana ɗaya. Za ku kamo daga cikin tumakinku ko awaki.


balle fa jinin Almasihu wanda ya miƙa kansa marar aibu ga Allah, ta wurin Madawwamin Ruhu, lalle zai tsarkake lamirinmu daga barin ibada marar tasiri, domin mu bauta wa Allah Rayayye.


Duk mutumin da yake da lahani na makanta, ko gurguntaka, ko rauni a fuska, ko gaɓar da ta fi wata,


Idan yana da wani lahani kamar gurguntaka ko makanta, ko kowane irin mugun lahani, to, kada ku miƙa shi hadaya ga Ubangiji Allahnku.


ya ba Isra'ilawa ka'idodin nan. Sa'ad da kowane mutum a cikinsu zai kawo sadaka ga Ubangiji, sai ya kawo sadakarsa daga cikin garkunansa na shanu, da na tumaki, da na awaki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ