ya faɗa wa Haruna, da shi da 'ya'yansa cewa, “Ku lura da tsarkakakkun abubuwa waɗanda Isra'ilawa suka keɓe domina, don kada ku ƙasƙantar da sunana mai tsarki. Ni ne Ubangiji.
“Har yanzu kuma duk sadakokin da Isra'ilawa suke bayarwa don hadaya ta ɗagawa da ta kaɗawa, na ba ka, kai da 'ya'yanka mata da maza, a kowane lokaci. Duk wanda yake da tsarki a gidanka zai iya ci.
Idan mutum ya ci amana, ya kuwa yi laifi ba da gangan ba, a kan tsarkakakkun abubuwa na Ubangiji, sai ya kawo rago marar lahani daga garken tumaki ga Ubangiji saboda yin hadaya don laifinsa. Za a kimanta ragon da tamanin kuɗi bisa ga ma'aunin azurfar da ake aiki da shi.