Amma Joshuwa ya ce wa mutanen, “Ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba, gama shi Allah mai tsarki ne, mai kishi kuma, ba kuwa zai gafarta laifofinku da zunubanku ba.
Sai dai ba zai kusaci labulen, ko ya tafi kusa da bagaden ba, domin yana da lahani, don kada ya ɓata wuraren yin sujada, gama ni ne Ubangiji, ni kuwa na tsarkake su.”