ya ce wa mutanen Isra'ila, “Duk Ba'isra'ile da kowane baƙo da yake zaune cikin Isra'ila, wanda ya ba da ɗaya daga cikin 'ya'yansa ga Molek, lalle ne a kashe shi. Mutanen ƙasar za su jajjefe shi da duwatsu.
Idan za ku yi tsoron Ubangiji, ku bauta masa, ku yi biyayya da maganarsa, ba za ku karya umarnin Ubangiji ba, idan kuma ku da sarkin da yake sarautarku za ku bi Ubangiji Allahnku, kome zai zamar muku daidai.
Duk wanda bai yi biyayya da shari'ar Allahnka ba, ko shari'ar sarki, sai a yi masa hukunci mai tsanani, ko na mutuwa, ko na kora, ko na ƙwace dukiyarsa, ko na kurkuku.”
A cikin kwarin ɗan Hinnon sun gina bagade, mai suna Tofet, don su miƙa 'ya'yansu mata da maza hadayar ƙonawa. Ni ban umarce su su yi haka ba, irin wannan abu ba shi a zuciyata.