Firistoci 2:2 - Littafi Mai Tsarki2 Zai kuma kawo hadayarsa a wurin 'ya'yan Haruna maza, firistoci. Zai ɗibi tāfi guda na lallausan garin da aka zuba wa mai da dukan lubban. Firist kuwa zai ƙona wannan a kan bagaden don tunawa, gama hadaya ta ƙonawa ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20202 yă kai wa ’ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci. Firist zai ɗiba gari mai laushin a tafin hannu da kuma man, tare da dukan turaren, yă ƙone wannan a sashen tunawa a kan bagade, hadaya ce da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Mutane suna yin abin da suka ga dama. Suna kashe bijimi domin hadaya, ko su yi hadaya da mutum. Sukan yi hadaya da ɗan rago, ko kuwa su karye wuyan kare. Sukan miƙa hadaya ta hatsi, ko kuwa su miƙa jinin alade. Suna miƙa turare, ko kuwa su yi addu'a ga gumaka. Suna jin daɗin al'amuran banƙyama a lokacin yin sujada.