Zan tallafe ku, ku zama jama'ata, ni kuwa in zama Allahnku. A sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya 'yanto ku daga wulakancin Masarawa.
Ka ce musu, ni Ubangiji Allah, na ce a ranar da na zaɓi Isra'ila na ta da hannuna, na rantse wa zuriyar Yakubu, na kuma bayyana kaina a gare su a ƙasar Masar, cewa ni ne Ubangiji Allahnsu,
Sai na ce musu, ‘Bari kowane ɗayanku ya yi watsi da abubuwan banƙyama da kuke jin daɗinsu, kada ku ƙazantar da kanku da gumakan Masarawa, gama ni ne Ubangiji Allahnku.’
Ubangiji kuma ya ce, “Don haka sai ku kiyaye umarnina, kada ku kiyaye dokoki na banƙyama waɗanda aka kiyaye kafin ku zo, kada ku ƙazantu da su. Ni ne Ubangiji Allahnku.”