“Idan 'yan'uwa suna zaune wuri ɗaya tare, in ɗayansu ya rasu bai haihu ba, to, kada matar marigayin ta auri wani baƙo wanda yake ba a cikin dangin mijin ba. Sai ɗan'uwan mijinta ya zo wurinta, ya aure ta, ya yi mata abin da ya kamaci ɗan'uwan miji ya yi.
“Malam, Musa dai ya rubuta mana, cewa idan ɗan'uwan mutum ya mutu, ya bar mata tasa ba ɗa, sai lalle mutumin ya auri matar, ya haifa wa ɗan'uwansa 'ya'ya.