10 Kada ya kwana da jikanyarsa gama zai zama ƙasƙanci a gare shi.
10 “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar ɗanka ko ’yar ’yarka, wannan zai ƙasƙantar da kai.
Kada ya kwana da 'yar'uwarsa, 'yar mahaifinsa, ko 'yar mahaifiyarsa, ko a gida ɗaya aka haife ta da shi, ko a wani gida dabam.
Kada ya kwana da 'yar matar mahaifinsa, wadda mahaifinsa ya haifa, tun da yake ita 'yar'uwarsa ce.