Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 17:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Sai firist ya yayyafa jinin a kan bagaden Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada. Zai ƙone kitsen don ya ba da ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Firist zai yayyafa jinin a bagaden Ubangiji, a ƙofar Tentin Sujada, yă kuma ƙone kitsen kamar ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 17:6
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Haihuwar fari ta saniya, ko ta tunkiya, ko ta akuya, ba za ka fanshe su ba, gama su halal ne. Sai kayayyafa jininsu a kan bagade, kitsensu kuma ka ƙone a kan bagaden ƙona hadayu, zai zama turare mai ƙanshi, mai daɗi ga Ubangiji.


Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadayarsa, ya yanka a bakin ƙofar alfarwa ta sujada. 'Ya'yan Haruna maza kuwa, firistoci, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi.


Za a ɗebe kitsenta duka kamar yadda akan ɗebe kitsen hadaya ta salama. Firist zai ƙona shi a kan bagaden don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Ta haka firist zai yi kafara dominsa, za a kuwa gafarta masa.


Firist kuwa zai ƙone su a bisa bagaden kamar hadayar abincin da akan ƙone don ya yi ƙanshi mai daɗi. Dukan kitse na Ubangiji ne.


Zai ɗibiya hannunsa a bisa kanta, ya yanka ta a gaban alfarwa ta sujada. 'Ya'yan Haruna, maza, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi.


Firist kuwa zai ƙone su a bisa bagaden kamar hadayar abincin da akan ƙone da wuta ga Ubangiji.


Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadayarsa, ya yanka a gaban alfarwa ta sujada. 'Ya'yan Haruna, maza kuwa, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi.


'Ya'yan Haruna, maza kuwa, za su ƙone su tare da hadayar ƙonawa da take bisa itacen da yake cikin wutar bagade, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.


Sa'an nan ka ƙone ragon duka a bisa bagaden don ya ba da ƙanshi. Wannan hadaya ta ƙonawa ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, wato hadayar da aka ƙone da wuta.


Ka cire dukan kitsen da yake rufe da kayan cikin, da kitsen da yake manne da hanta, da wanda yake manne a ƙoda biyu ɗin. Ka ƙone su a bisa bagaden.


Manufar wannan umarni ce domin Isra'ilawa su riƙa kawo hadayunsu, waɗanda sukan yi a filin saura ga Ubangiji a wurin firist a ƙofar alfarwa ta sujada. Sai su yanka hadayu na salama ga Ubangiji.


“Amma Lawiyawan da suke firistoci daga zuriyar Zadok, waɗanda suka lura da Wuri Mai Tsarki sa'ad da mutanen Isra'ila suka karkace, suka bar bina, su ne za su zo kusa da ni, su yi mini hidima, za su kusace ni domin su miƙa hadaya ta kitse da jini, ni Ubangiji Allah na faɗa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ