Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 17:4 - Littafi Mai Tsarki

4 bai kuwa kawo shi a ƙofar alfarwa ta sujada don ya miƙa shi sadaka ga Ubangiji a gaban alfarwa ta sujada ba, alhakin jinin da ya zubar yana bisa kansa, za a fitar da wannan mutum daga cikin jama'arsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 a maimakon kawo shi a matsayin hadaya ga Ubangiji a gaban tabanakul na Ubangiji, za a ɗauki wannan mutum a matsayi mai laifin zub da jini, ya zub da jini, kuma dole a raba shi da mutanensa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 17:4
30 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yesu ya ce masa, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina.


Ni ne ƙofar. Kowa ya shiga ta wurina zai sami ceto, ya kai ya kawo, ya kuma yi kiwo.


Don haka Yesu ya sāke ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, ni ne ƙofar tumakin.


“Gama a kan dutsena ne mai tsarki, wato a bisa ƙwanƙolin dutsen Isra'ila, dukan mutanen Isra'ila za su bauta mini a ƙasar, a nan ne zan karɓe su. A nan kuma zan nemi sadake-sada-kenku, da hadayunku mafi kyau.


“Mutane suna yin abin da suka ga dama. Suna kashe bijimi domin hadaya, ko su yi hadaya da mutum. Sukan yi hadaya da ɗan rago, ko kuwa su karye wuyan kare. Sukan miƙa hadaya ta hatsi, ko kuwa su miƙa jinin alade. Suna miƙa turare, ko kuwa su yi addu'a ga gumaka. Suna jin daɗin al'amuran banƙyama a lokacin yin sujada.


Kowane ɗa namiji da bai yi kaciya ba, wato wanda bai yi kaciyar loɓarsa ba, za a fitar da shi daga jama'arsa, don ya ta da alkawarina.”


Shari'a fa, an shigo da ita ne, don laifi yă haɓaka. Amma a inda zunubi ya haɓaka, alherin Allah ma ya fi haɓaka ƙwarai da gaske.


Lalle fa zunubi yana nan a duniya tun ba a ba da Shari'a ba, sai dai inda ba shari'a, ba a lasafta zunubi.


Haka kuma Dawuda ya yi maganar albarkar da aka yi wa mutumin da Allah yake lasafta adalci a gare shi, ba don ya yi aikin lada ba,


Mai farin ciki ne wanda Ubangiji bai zarge shi a kan wani laifi ba, Wanda ba algus ko kaɗan a cikinsa.


Idan mutum ya kwana da mace a lokacin hailarta, duka biyunsu za a kore su daga cikin jama'arsu, gama sun karya ka'idodi a kan rashi tsarki.


In kuma mace ta yi ƙoƙari har ta kwana da dabba, sai a kashe matar tare da dabbar, alhakin jininsu yana wuyansu.


Ni kaina zan yi gāba da wannan mutum, in raba shi da jama'arsa domin ya ba Molek ɗaya daga cikin 'ya'yansa, gama ya ƙazantar da alfarwa ta sujada, ya ƙasƙantar da sunana mai tsarki.


Duk wanda ya aikata abu ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa masu banƙyaman nan za a raba shi da jama'a.


Gama ran dukan nama yana cikin jininsa, saboda haka Ubangiji ya faɗa wa mutanen Isra'ila, cewa, faufau ba za su ci jinin kowace dabba ba, gama ran kowace dabba yana cikin jininta. Duk wanda kuwa ya ci shi, za a raba shi da jama'a.


Idan wani Ba'isra'ile, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu ya ci jini, Ubangiji zai yi gāba da wannan mutum da ya ci jinin ya fitar da shi daga cikin jama'a.


Idan aka ci naman hadayarsa ta salama a rana ta uku, ba za a karɓi wanda ya ba da hadayar har ya sami fa'idar hadayar ba, naman zai zama abin ƙyama, duk wanda ya ci ya yi laifi.


Idan sadakarsa ta hadayar ƙonawa ce daga cikin garken shanu, sai ya ba da namiji marar lahani, zai miƙa shi a ƙofar alfarwa ta sujada domin sadakar ta zama abar karɓa a gaban Ubangiji.


Amma kada a iske yisti a gidajenku har kwana bakwai, gama idan wani ya ci abin da aka sa wa yisti za a fitar da shi daga cikin taron jama'ar Isra'ila, ko shi baƙo ne ko kuwa haifaffen ƙasar.


“Za ku yi kwana bakwai kuna cin abinci marar yisti. A rana ta fari za ku fitar da yisti daga cikin gidajenku, gama duk wanda ya ci abin da aka sa wa yisti tun daga rana ta fari har zuwa ta bakwai za a fitar da shi daga cikin Isra'ila.


Idan Ba'isra'ile ya yanka sa, ko ɗan rago, ko akuya a cikin zango, ko a bayan zango,


Manufar wannan umarni ce domin Isra'ilawa su riƙa kawo hadayunsu, waɗanda sukan yi a filin saura ga Ubangiji a wurin firist a ƙofar alfarwa ta sujada. Sai su yanka hadayu na salama ga Ubangiji.


amma bai kawo ta a ƙofar alfarwa ta sujada, ya miƙa ta ga Ubangiji ba, sai a fitar da wannan mutum daga cikin jama'a.


Duk wanda ya yi wani irinsa ko kuwa ya shafa wa wani, za a raba shi da jama'arsa’ ”


Duk wanda ya yi irin turaren nan don amfanin kansa, za a raba shi da jama'arsa.”


Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadayarsa, ya yanka a bakin ƙofar alfarwa ta sujada. 'Ya'yan Haruna maza kuwa, firistoci, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi.


Ya Ubangiji, ka kuɓutar da jama'arka, Isra'ila, wadda ka fansa, kada ka bar alhakin jinin marar laifin nan ya kama jama'arka, Isra'ila. Ka gafarta musu alhakin wannan jini.’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ