Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 16:34 - Littafi Mai Tsarki

34 Wannan zai zama dawwamammiyar farilla a gare su. Za a riƙa yin kafara domin jama'ar Isra'ila saboda zunubansu duka sau ɗaya a shekara. Sai Musa ya aikata kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

34 “Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce gare ku. Za a riƙa yin kafara sau ɗaya a shekara saboda dukan zunuban Isra’ilawa.” Aka kuma yi haka, yadda Ubangiji ya umarci Musa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 16:34
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma na biyun, sai babban firist kaɗai yake shiga, shi ma kuwa sai sau ɗaya a shekara, sai kuma da jini wanda yakan miƙa saboda kansa, da kuma kurakuran jama'a.


Ba kuwa domin ya riƙa miƙa kansa hadaya a kai a kai ba ne, kamar yadda babban firist yake shiga Wuri Mafi Tsarki a kowace shekara da jinin da ba nasa ba ne.


Sau ɗaya a shekara Haruna zai yi kafara a bisa zankayensa. Zai yi kafara a bisansa da jinin hadaya don zunubi ta yin kafara. Za a riƙa yin wannan dukan zamananku, gama bagaden mai tsarki ne ga Ubangiji.”


Gama ta hadaya guda kawai ya kammala waɗanda aka tsarkake har abada.


Amma a game da irin waɗannan hadayu, akan tuna da zunubai a kowace shekara,


Za a yi tsattsarkan taro a rana ta goma ga watan bakwai domin yin sujada. Ba za a ci abinci ba, ba kuwa za a yi aiki ba.


Wannan ka'ida ta shafi dukan zuriyarsu a duk inda suke.


Za a ajiye ta a cikin alfarwar a gaban labule na wurin shaida. Haruna da 'ya'yansa za su lura da ita daga safiya har maraice. Wannan zai zama ka'ida har abada ga Isra'ilawa.”


Ba za su yi aiki a wannan rana ba, gama rana ce ta yin kafara dominsu.


Da Musa ya duba dukan aikin, ga shi kuwa, sun yi shi daidai, kamar yadda Ubangiji ya umarta, sai Musa ya sa musu albarka.


Ba za a ci kitse ko jinin ba a wuraren zamanku. Wannan doka madawwamiya ce.


Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Faɗa wa ɗan'uwanka Haruna kada ya riƙa shiga Wuri Mafi Tsarki bayan labule ko yaushe, wato, a gaban murfi wanda yake bisa akwatin alkawari, domin kada ya mutu, gama zan bayyana a cikin girgije a kan murfin.


Sai Musa ya yi magana da Isra'ilawa, suka kuwa fito masa da mutumin da ya yi saɓon a bayan zangon. Suka jajjefe shi da duwatsu. Haka Isra'ilawa suka aikata yadda Ubangiji ya umarci Musa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ