Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 16:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Sai ya ɗibi jinin bijimin, ya yayyafa da yatsansa a gefen gabas na murfin, zai kuma yayyafa jinin a gaban murfin sau bakwai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Zai ɗibi jinin bijimin da yatsarsa yă yayyafa a gaban murfin kafarar; sa’an nan yă yayyafa jinin da yatsarsa sau bakwai a gaban murfin kafarar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 16:14
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ba kuwa domin ya riƙa miƙa kansa hadaya a kai a kai ba ne, kamar yadda babban firist yake shiga Wuri Mafi Tsarki a kowace shekara da jinin da ba nasa ba ne.


To, jinin awaki ne fa da na bijimai, da kuma tokar karsana da ake yayyafa wa waɗanda suka ƙazantu, suke tsarkake su da tsabtacewar jiki,


domin ba mai yiwuwa ba ne jinin bijimai da na awaki ya ɗauke zunubi.


Amma na biyun, sai babban firist kaɗai yake shiga, shi ma kuwa sai sau ɗaya a shekara, sai kuma da jini wanda yakan miƙa saboda kansa, da kuma kurakuran jama'a.


Ya yayyafa wa bagaden mai sau bakwai, ya kuma shafa wa bagaden da dukan kayayyakinsa, da daron da gammonsa, don ya tsarkake su.


Sa'an nan ya tsoma yatsansa a cikin jinin ya yayyafa shi sau bakwai a gaban Ubangiji, a gaban labulen.


Kun iso wurin Yesu, matsakancin sabon alkawari, da kuma wurin jinin nan na tsarkakewa, wanda yake yin mafificiyar magana fiye da na Habila.


Saboda haka, ya 'yan'uwa, tun da muke da amincewar shiga Wuri Mafi Tsarki, ta wurin jinin Yesu,


Haka kuma, ya yayyafa jinin ga alfarwar nan, da dukan kayanta na yin hidima.


Zai kuma yayyafa jinin da yatsansa har sau bakwai a kan bagaden, ya tsabtace shi, ya tsarkake shi daga ƙazantar jama'ar Isra'ila.


Ele'azara, firist, kuwa zai ɗibi jininta da yatsansa, ya yayyafa sau bakwai a wajen alfarwar ta sujada.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ