Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 15:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Sa'ad da mai ɗigar ya warke, sai ya ƙidaya ranaku bakwai don tsarkakewarsa, ya wanke tufafinsa, ya yi wanka a ruwa mai gudu, zai tsarkaka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 “ ‘Sa’ad da aka tsabtacce mai ɗigar, zai ɗauki kwana bakwai don tsabtaccewarsa; dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka mai tsabta, zai kuwa zama tsarkakakke.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 15:13
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Shi kuwa wanda za a tsarkake, sai ya wanke tufafinsa, ya aske dukan gashinsa, ya yi wanka da ruwa, zai kuwa tsarkaka. Bayan wannan zai shiga zango, amma kada ya shiga cikin alfarwarsa har kwana bakwai.


Ba za ku fita daga cikin alfarwa ta sujada ba har kwana bakwai, wato, sai kwanakin keɓewarku sun cika, gama keɓewarku za ta ɗauki kwana bakwai.


Bayan da hailarta ta tsaya, za ta ƙidaya kwanaki bakwai, bayan haka za ta tsarkaka.


Duk wanda ya taɓa gadonsa, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.


da kuma Yesu Almasihu Amintaccen Mashaidi, na farko a cikin masu tashi daga matattu, mai mulkin sarakunan duniya. Ɗaukaka da mulki su tabbata har abada abadin ga wanda yake ƙaunarmu, ya kuma ɓalle mana ƙangin zunubanmu ta wurin jininsa,


Ku kusaci Allah, shi ma zai kusace ku. Ku tsarkake al'amuranku, ya ku masu zunubi. Ku kuma tsarkake zukattanku, ya ku masu zuciya biyu.


Ya ku ƙaunatattu, tun da aka yi mana waɗannan alkawarai, sai mu tsarkake kanmu daga kowace irin ƙazanta ta jiki ko ta zuci, da bangirma ga Allah mu kamalta a cikin tsarki.


Zan shafe dukan laifin da suka yi mini, in kuma gafarta musu dukan zunubansu da tayarwar da suka yi mini.


Amma ubangiji ya ce wa Musa, “Da a ce mahaifinta ne ya tofa mata yau a fuskarta, ba za ta ji kunya har kwana bakwai ba? Bari a fitar da ita a bayan zangon kwana bakwai, bayan haka a shigar da ita.”


A rana ta takwas zai kawo 'yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya marasa lahani da 'yar tunkiya bana ɗaya marar lahani, da hadaya ta gari rabin garwar gari mai laushi karɓaɓɓe da man zaitun, da rabin moɗa na mai.


A kan rana ta takwas, Musa ya kirawo Haruna, da 'ya'yansa maza, da dattawan Isra'ila.


Kwana bakwai za ka ɗauka na yin kafara don bagaden, ka keɓe shi, haka kuwa bagaden zai zama mafi tsarki. Duk abin da ya taɓa bagaden zai tsarkaka.”


“Haka nan za ka yi wa Haruna da 'ya'yansa maza bisa ga dukan abin da na umarce ka. Kwana bakwai za ka ɗauka domin keɓewarsu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ