Abin da ba shi yiwuwa Shari'a ta yi domin ta kasa saboda halin ɗan adam, Allah ya yi shi, wato ya ka da zunubi a cikin jiki, da ya aiko da Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, domin kawar da zunubi.
Amma idan ɗan rago ya fi ƙarfinta, sai ta kawo kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu, ɗaya don hadaya ta ƙonawa, ɗayan kuwa don yin hadaya don zunubi. Firist kuwa zai yi kafara dominta, za ta kuwa tsarkaka.
Amma idan 'yar tunkiyar ta fi ƙarfinsa, sai ya kawo kurciyoyi biyu ko 'yan tattabarai biyu don yin hadaya ga Ubangiji saboda laifin da ya yi. Ɗaya za ta zama ta yin hadaya don laifi, ɗayan kuwa don yin hadaya ta ƙonawa.
ɗaya domin hadaya don zunubi, ɗaya kuma don hadaya ta ƙonawa tare da hadaya ta gari. Firist ɗin kuma zai yi kafara a gaban Ubangiji domin wanda ake tsarkakewar.