9 Sa'ad da cutar kuturta ta kama mutum, sai a kai shi wurin firist.
9 “Sa’ad da wani yana da cutar fatar jiki, dole a kawo shi ga firist.
Idan mutum yana da kumburi a fatar jikinsa, ko ɓamɓaroki ko tabo, har ya zama kamar cutar kuturta, sai a kai shi wurin Haruna, firist, ko ɗaya daga cikin zuriyarsa, firistoci.
Firist zai duba shi, idan ɓamɓaroki ya yaɗu a fatar, sai firist ya hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, ba ɓamɓaroki ba ne, kuturta ce.
Firist kuwa ya dudduba shi, in akwai kumburi a fatar jikin mutum wanda ya rikiɗar da gashin wurin ya zama fari, in kuma akwai sabon miki a kumburin,