kuna ceton waɗansu kuna fizgo su daga wuta. Waɗansu kuma ku ji tausayinsu, amma tare da tsoro kuna ƙyamar ko da tufafin da halinsu na mutuntaka ya ƙazantar.
Kin ɗauki waɗansu rigunanki, kika yi wa kanki masujadai masu ado, sa'an nan kika yi karuwanci a cikinsu, irin abin da ba a taɓa yi ba, ba kuwa za a yi ba nan gaba.
Dukanmu muka cika da zunubi har ayyukanmu mafi kyau ƙazamai ne duka. Saboda zunubanmu, muka zama kamar busassun ganyaye waɗanda iska take faucewa ta tafi da su.
Wannan ita ce dokar da za a bi a kan cutar kuturtar rigar ulu ko ta lilin, ko cutar kuturta ta tariyar zaren, ko ta waɗarin, ko kuma ta kan kowane abu da aka yi da fata, don a tabbatar tsattsarka ne, ko marar tsarki ne.