sai firist ya dudduba cutar, in ya ga zurfin cutar ya zarce fatar, gashin kuma da yake wurin ya zama rawaya, siriri kuma, firist zai hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, miki ne, ciwon da za a iya ɗauka ne.
A rana ta bakwai firist zai dudduba mikin, idan mikin bai bazu ba, zurfinsa kuma bai zarce fatar ba, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne, sai mutumin ya wanke tufafinsa, ya tsarkaka ke nan.