Shari'ar shugabannin ƙasar ta cin hanci ce. Firistocinta suna koyarwa don neman riba, Haka kuma annabawa suna annabci don neman kuɗi. Duk da haka suna dogara ga Ubangiji, suna cewa, “Ai, Ubangiji yana tsakiyarmu, Ba masifar da za ta same mu.”
Kun shiga uku! Kun ce mugunta ita ce nagarta, nagarta kuwa mugunta. Kun mai da duhu shi ne haske, haske kuwa duhu. Kun mai da abin da yake mai ɗaci mai zaƙi, mai zaƙi kuwa kun maishe shi mai ɗaci.
kowace irin addu'a, kowane irin roƙo da kowane mutum, ko jama'ar Isra'ila suka yi, ko wannensu yana sane da irin wahalarsa, da baƙin cikinsa, ya kuwa ɗaga hannunsa wajen wannan Haikali,
Sai sarki Yerobowam ya yi shawara, ya siffata 'yan maruƙa biyu da zinariya. Sa'an nan ya ce wa jama'arsa, “Zuwanku Urushalima ya isa, yanzu ga allolinku, ya Isra'ilawa, waɗanda suka fito da ku daga ƙasar Masar.”
sai ka kasa kunne ga addu'arsu. Idan ɗaya daga cikin jama'arka Isra'ila ya matsu a zuciyarsa, ya ɗaga hannuwansa sama yana addu'a wajen wannan Haikali,
Amma idan tabon ya tsaya a wuri ɗaya, bai bazu a fatar jikin ba, ya kuma dushe, to, kumburi ne na ƙunar, firist zai hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne, gama tabon ƙuna ne.
sai firist ya dudduba cutar, in ya ga zurfin cutar ya zarce fatar, gashin kuma da yake wurin ya zama rawaya, siriri kuma, firist zai hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, miki ne, ciwon da za a iya ɗauka ne.
Ubangiji ya ce, “Ya kai ɗan mutum, sai ka ɗauki takobi mai kaifi, ka more shi kamar askar wanzami, ka aske kanka da gemunka. Ka auna gashin da ma'auni, don ka raba shi kashi uku.