16 Idan kuma sabon mikin ya juya, ya rikiɗa ya zama fari, zai tafi wurin firist.
16 A ce sabon mikin ya canja ya juya fari, dole yă je wurin firist.
Wata rana Yesu na ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutum wanda kuturta ta ci ƙarfinsa ya zo. Da ya ga Yesu ya fāɗi a gabansa, ya roƙe shi ya ce, “Ya Ubangiji, in dai ka yarda kana da ikon tsarkake ni.”
Sai firist ya dudduba sabon mikin ya hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, sabon miki fa marar tsarki ne, gama kuturta ce.
Firist ɗin zai dudduba shi, idan cutar ta rikiɗa ta zama fara, sai firist ya hurta, cewa, mutumin tsarkakakke ne, gama ya tsarkaka.