Amma idan ɗan rago ya fi ƙarfinta, sai ta kawo kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu, ɗaya don hadaya ta ƙonawa, ɗayan kuwa don yin hadaya don zunubi. Firist kuwa zai yi kafara dominta, za ta kuwa tsarkaka.
Idan mutum yana da kumburi a fatar jikinsa, ko ɓamɓaroki ko tabo, har ya zama kamar cutar kuturta, sai a kai shi wurin Haruna, firist, ko ɗaya daga cikin zuriyarsa, firistoci.
Wata rana Yesu na ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutum wanda kuturta ta ci ƙarfinsa ya zo. Da ya ga Yesu ya fāɗi a gabansa, ya roƙe shi ya ce, “Ya Ubangiji, in dai ka yarda kana da ikon tsarkake ni.”