Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 12:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Amma idan ɗan rago ya fi ƙarfinta, sai ta kawo kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu, ɗaya don hadaya ta ƙonawa, ɗayan kuwa don yin hadaya don zunubi. Firist kuwa zai yi kafara dominta, za ta kuwa tsarkaka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 In ba za tă iya kawo ɗan rago ba, sai ta kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu, ɗaya domin hadaya ta ƙonawa ɗayan kuma domin hadaya don zunubi. Ta haka firist zai yi kafara dominta, za tă kuwa zama tsabtacciya.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 12:8
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma idan 'yar tunkiyar ta fi ƙarfinsa, sai ya kawo kurciyoyi biyu ko 'yan tattabarai biyu don yin hadaya ga Ubangiji saboda laifin da ya yi. Ɗaya za ta zama ta yin hadaya don laifi, ɗayan kuwa don yin hadaya ta ƙonawa.


Firist ɗin zai ƙona kitsen duka a bisa bagaden kamar yadda akan yi da kitsen hadaya ta salama, ta haka firist zai yi kafara domin zunubin shugaban, za a kuwa gafarta masa.


da kuma kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu yadda dai ya iya. Ɗayan domin hadaya don zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa.


Idan kuma hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji daga cikin tsuntsaye ne, sai ya kawo kurciyoyi, ko 'yan tattabarai.


Domin kun san alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu, ko da yake shi mawadaci ne, sai ya zama matalauci sabili da ku, domin ta wurin talaucinsa ku wadata.


A rana ta takwas sai ta kawo 'yan kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai, a wurin firist a ƙofar alfarwa ta sujada.


A kan rana ta takwas zai kawo kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada, ya ba firist.


Sai Yesu ya shiga Haikalin ya kakkori dukkan masu saye da sayarwa a ciki, ya birkice teburorin 'yan canjin kuɗi da kujerun masu sayar da tattabarai.


Sai ya miƙa ga Ubangiji, ya yi kafara dominta, za ta kuwa tsarkaka. Wannan shi ne abin da ya wajaba ga wanda ta haifi ɗa ko 'ya.


Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan ka'idodi.


Amma idan matalauci ne, har ba zai iya samun waɗannan abubuwa ba, sai ya kawo ɗan rago ɗaya domin hadaya don laifi, a yi hadaya ta kaɗawa, a yi kafara dominsa. Ya kuma kawo humushin garwa na gari mai laushi kwaɓaɓɓe da man zaitun don yin hadaya ta gari, da rabin moɗa na mai,


Amma idan har kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu sun fi ƙarfinsa don yin hadaya saboda laifinsa, sai ya kawo humushin garwar gari mai laushi don yin hadaya saboda laifinsa. Ba zai zuba mai ko lubban a garin ba, gama hadaya ce don laifi.


Sai firist ya yi hadaya da su, ɗaya don hadayar zunubi, ɗaya kuma don hadaya ta ƙonawa. Firist ɗin zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji domin ɗigarsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ