Ga abin da nake nufi. Shari'ar nan, wadda ta zo shekara arbaminya da talatin daga baya, ba ta shafe alkawarin nan da Allah ya tabbatar tun tuni ba, har da za ta wofinta shi.
To, mun sani duk abin da Shari'a ta ce, ya shafi waɗanda suke ƙarƙashinta ne, don a tuƙe hanzarin kowa, duk duniya kuma tă sani ƙarƙashin hukuncin Allah take.
Sai kuma waɗansu mutane suka zo daga Yahudiya suna koya wa 'yan'uwa, suna cewa, “In ba an yi muku kaciya kamar yadda al'adar Musa take ba, ba dama ku sami ceto.”
Haka kuma za ku yi da 'ya'yan farin shanunku, da na awakinku, da na tumakinku. Ɗan farin zai yi kwana bakwai tare da uwar, amma a rana ta takwas za ku ba ni shi.
Sa'an nan kuma sai ta ci gaba da zama cikin jinin har kwana talatin da uku. A lokacin ba za ta taɓa kowane tsattsarkan abu ba, ba za ta shiga wurin yin sujada ba, har kwanakin tsarkakewarta su cika.