1 Ubangiji ya ba Musa ka'idodin nan domin jama'ar Isra'ila.
1 Ubangiji ya ce wa Musa,
Dole ku lura ku bambanta tsakanin masu tsarki, da marasa tsarki, da tsakanin dabbobin da za a ci, da waɗanda ba za a ci ba.
Idan mace ta yi ciki, ta haifi ɗa namiji, to, za ta zama marar tsarki har kwana bakwai, kamar cikin kwanakin hailarta.
Ko kuma idan ya taɓa kowace irin ƙazantar mutum wadda akan ƙazantu da ita, ba da saninsa ba, amma in daga baya ya sani, to, laifi ya kama shi.
Idan wani mutum ya taɓa abu marar tsarki, ko mutum ne, ko dabba ce, ko wani abu na banƙyama, ya kuma ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji, za a raba wannan mutum da mutanensa.
Da kwanakin tsarkakewarsu suka cika bisa ga Shari'ar Musa, suka kawo shi Urushalima, su miƙa shi ga Ubangiji