Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 11:40 - Littafi Mai Tsarki

40 Wanda kuwa ya ci mushen sai ya wanke tufafinsa, ya ƙazantu har zuwa maraice. Haka kuma shi wanda ya ɗauki mushen zai wanke tufafinsa ya kuma ƙazantu har zuwa maraice.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

40 Duk wanda ya ci wani sashe na gawar dole yă wanke rigunansa, kuma zai ƙazantu har yamma. Duk wanda ya ɗauki gawar dole yă wanke rigunansa, zai kuwa ƙazantu har yamma.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 11:40
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Firistoci ba za su ci mushen kowane irin tsuntsu ko dabba ba, ba kuma za su ci waɗanda wata dabba ta kashe ba.”


Kada ya ci abin da ya mutu mushe, ko abin da namomin jeji suka yayyaga, don kada ya ƙazantar da kansa. Ni ne Ubangiji.


“Kada ku ci mushe. Amma mai yiwuwa ne ku ba baren da yake zaune a garuruwanku, ko kuma ku sayar wa baƙo. Gama ku jama'a ce keɓaɓɓiya ga Ubangiji Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya a madarar uwarsa.”


Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah, ban taɓa ƙazantar da kaina ba. Tun daga ƙuruciyata har zuwa yau, ban taɓa cin mushe ba, ko abin da namomin jeji suka kashe. Ƙazantaccen nama bai taɓa shiga bakina ba.”


In kuwa muna zaune a haske, kamar yadda shi yake cikin haske, muna tarayya da juna ke nan, jinin Yesu Ɗansa kuma yana tsarkake mu daga dukkan zunubi.


Ba dama ku sha a ƙoƙon Ubangiji, ku kuma sha a na aljannu. Ba dama ku ci abinci a teburin Ubangiji, ku kuma ci a na aljannu.


Waɗansunku ma dā haka suke, amma an wanke ku, an tsarkake ku, an kuma kuɓutar da ku, da sunan Ubangiji Yesu Almasihu, da kuma Ruhun Allahnmu.


“A ran nan za a buɗe maɓuɓɓuga don wanke zuriyar Dawuda da mazaunan Urushalima daga zunubi da rashin tsarki.


Zan yayyafa muku tsabtataccen ruwa, za ku kuwa tsarkaka daga dukan ƙazantarku, da kuma daga dukan gumakanku.


Ku yi wanka sarai. Ku daina aikata dukan wannan mugun abu da na ga kuna aikatawa. I, ku daina aikata mugunta.


A kan rana ta uku da ta bakwai kuma, wanda yake da tsarki zai yayyafa wa marar tsarkin ruwa, ya tsarkake shi. Sai mutumin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, da maraice kuwa zai tsarkaka.


Shi wanda ya ƙone su, zai wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, bayan haka ya iya komawa zangon.


Shi wanda ya kore bunsurun Azazel, sai ya wanke tufafinsa ya yi wanka da ruwa, bayan haka yana iya komawa cikin zango.


Wanda duk ya taɓa waɗannan abubuwa zai ƙazantu, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.


Wanda kuma ya ɗauki mushensu, sai ya wanke tufafinsa, ya zama ƙazantacce har zuwa maraice.


Duk wanda kuma ya ɗauki mushensu dole ne ya wanke tufafinsa, amma zai ƙazantu har zuwa maraice.


“Za ku zama keɓaɓɓun mutane a gare ni. Kada ku ci dabbar da naman jeji ya yayyage shi, sai ku jefa wa karnuka.”


Idan kuma wata dabbar da kuke ci ta mutu, wanda duk ya taɓa mushenta zai ƙazantu har zuwa maraice.


Duk wanda ya shiga gidan bayan da an rufe shi, zai ƙazantu har maraice.


Sai firist ya yi hadaya da su, ɗaya don hadayar zunubi, ɗaya kuma don hadaya ta ƙonawa. Firist ɗin zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji domin ɗigarsa.


duk mutumin da ya taɓa kowane irin abu haka, zai ƙazantu har maraice, ba kuwa zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwan nan ba, sai ya yi wanka da ruwa tukuna.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ