To, waɗannan Yahudawa kam, sun fi na Tasalonika dattaku, domin sun karɓi Maganar hannu biyu biyu, suna ta nazarin Littattafai kowace rana, su ga ko abin haka yake.
Ba kuma za ku ci alade ba, ko da yake yana da rababben kofato, amma ba ya tuƙa. Haram ne shi a gare ku. Kada ku ci naman irin waɗannan dabbobi, ko ku taɓa mushensu.