In da haka ne, ashe, da sai lalle ya yi ta shan wuya a kai a kai ke nan, tun daga farkon duniya. Amma a yanzu ya bayyana sau ɗaya tak, a ƙarshen zamanai, domin ya kawar da zunubi ta wurin miƙa kansa hadaya.
Idan mutuwarku tare da Almasihu ta 'yanta ku daga al'adun duniyar nan, me ya sa kuke zama har yanzu kamar ku na duniya ne? Don me kuke bin dokokin da aka yi bisa ga umarnin 'yan adam da koyarwarsu,
“Daga cikin zuriyar Haruna wanda yake kuturu, ko mai ɗiga, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwa ba, sai lokacin da ya tsarkaka. Duk wanda ya taɓa wani abu marar tsarki na mamaci, ko wanda maniyyinsa yake ɗiga,
Ko kuma idan mutum ya taɓa kowane abin da yake haram ko mushen haramtacciyar dabba ta jeji ko ta gida, ko mushen haramtaccen abin da yake rarrafe, zai zama da laifi, ko da bai sani ba.
Idan wani mutum ya taɓa abu marar tsarki, ko mutum ne, ko dabba ce, ko wani abu na banƙyama, ya kuma ci naman hadaya ta salama ga Ubangiji, za a raba wannan mutum da mutanensa.
Duk wanda ya taɓa kowane abin da yake ƙarƙashin sirdin zai ƙazantu har maraice, duk kuma wanda ya ɗauki wannan abu, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, zai ƙazantu har maraice.
Sai firist ya yi hadaya da su, ɗaya don hadayar zunubi, ɗaya kuma don hadaya ta ƙonawa. Firist ɗin zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji domin ɗigarsa.
duk mutumin da ya taɓa kowane irin abu haka, zai ƙazantu har maraice, ba kuwa zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwan nan ba, sai ya yi wanka da ruwa tukuna.