Amma mutanen nan sukan kushe duk abin da ba su fahinta ba, saboda abubuwan da suka sani bisa ga jiki suna kamar dabbobi marasa hankali, su ne kuwa sanadin halakarsu.
“Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu; ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗaya, ko kuwa ya amince wa ɗayan, ya raina ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.”
Ka cece ni daga gare su da ikonka, Ka cece ni daga waɗanda suke da duk abin da suke so a duniyan nan, Ka hukunta su da wahalar da ka shirya musu, Ka sa har 'ya'yansu, su ma, ta ishe su, Wahalar da ta ragu kuma, ta sami jikokinsu!
Duk abin da yake tafiya a kan daginsa daga cikin dabbobin da suke da ƙafa huɗu, haram ne a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu har zuwa maraice.