Firistoci 10:14 - Littafi Mai Tsarki14 Amma ƙirjin da aka yi hadayar ta kaɗawa da shi da cinyar da aka miƙa, za ka ci su a kowane tsabtataccen wuri, da kai da 'ya'yanka mata da maza, gama wannan ne rabon da aka ba ku, daga hadayun salama na Isra'ilwa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202014 Amma kai da ’ya’yanka maza da mata za su iya ci ƙirjin da aka kaɗa, da kuma cinyar da aka miƙa. Ku ci su a wuri mai tsabta; an ba da su gare ku da kuma ’ya’yanku a matsayin rabo daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan ya ce mini, “Ɗakunan da suke wajen kudu da na wajen arewa gaban farfajiya, su ne tsarkakan ɗakuna inda firistoci waɗanda suke kusatar Ubangiji za su ci hadayu mafi tsarki. A nan kuma za su ajiye hadayu mafi tsarki, wato hadaya ta gari, da hadaya domin zunubi, da hadaya domin laifi, gama wurin tsattsarka ne.