Firistoci 10:13 - Littafi Mai Tsarki13 Za ku ci shi a wuri mai tsarki gama naka rabo ke nan da na 'ya'yanka maza daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji, gama haka Ubangiji ya umarce ni. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202013 Ku ci shi a tsattsarkan wuri, gama rabonka ne da na ’ya’yanka daga cikin hadayun da akan ƙone da wuta ga Ubangiji; gama haka aka umarce ni. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan ya ce mini, “Ɗakunan da suke wajen kudu da na wajen arewa gaban farfajiya, su ne tsarkakan ɗakuna inda firistoci waɗanda suke kusatar Ubangiji za su ci hadayu mafi tsarki. A nan kuma za su ajiye hadayu mafi tsarki, wato hadaya ta gari, da hadaya domin zunubi, da hadaya domin laifi, gama wurin tsattsarka ne.