Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 1:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Sa'an nan 'ya'yan Haruna maza, firistoci, za su hura wuta a bisa bagaden, su jera itace daidai a wutar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 ’Ya’yan Haruna maza waɗanda suke firistoci za su hura wuta a bagade, su kuma shirya itace a kan wutar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 1:7
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'ad da suka zo wurin da Allah ya faɗa masa, sai Ibrahim ya gina bagade a can, ya jera itace a kai. Ya ɗaure Ishaku ɗansa, ya sa shi a bisa itacen bagaden.


“Da ma wani daga cikinku ya rufe ƙofofin Haikali don kada ku shiga, ku hura wuta marar amfani a bisa bagadena! Ban ji daɗinku ba. Ba zan karɓi hadayun da kuke kawo mini ba,” in ji Ubangiji Mai Runduna.


Na kuma shirya yadda za a tara itace domin yin hadaya a kan kari, da kuma lokacin da za a kawo nunan fari. “Ya Allahna, ka tuna da ni, ka yi mini alheri.”


Sa'ad da Sulemanu ya gama yin addu'arsa, sai wuta ta sauko daga sama, ta cinye hadayar ƙonawa tare da sauran hadayu, darajar Ubangiji kuma ta cika Haikalin.


Dawuda ya gina wa Ubangiji bagade a wurin, ya miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama. Sai ya yi roƙo ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya amsa masa ta wurin wutar da ta sauko daga sama a bisa bagaden hadayar ta ƙonawa.


Wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji, ta ƙone hadaya ta ƙonawa da kitsen a bisa bagaden. Da jama'a duka suka gani, suka yi ihu, suka fāɗi rubda ciki suka yi sujada.


Ya shirya itacen wuta, ya yanyanka bijimin gunduwa gunduwa, ya shimfiɗa shi bisa itacen. Sa'an nan ya ce a cika tuluna huɗu da ruwa, a kwarara a kan hadaya ta ƙonawar da kan itacen.


ɗan Elkana, ɗan Yeroham, ɗan Eliyab, ɗan Mahat,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ