Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Firistoci 1:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Sa'an nan zai yanka ɗan bijimin a gaban Ubangiji. 'Ya'yan Haruna maza, firistoci, za su miƙa jinin a bagaden da yake a ƙofar alfarwa ta sujada za su kuma yayyafa jinin a kewaye da shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Zai yanka ɗan bijimin a gaban Ubangiji, Haruna kuwa da ’ya’yansa maza firist, za su kawo jinin su kuma yafa shi a kan bagaden a kowane gefe a mashigin Tentin Sujada.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Firistoci 1:5
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadayarsa, ya yanka a gaban alfarwa ta sujada. 'Ya'yan Haruna, maza kuwa, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi.


Zai yanka shi a arewacin bagaden a gaban Ubangiji. 'Ya'yan Haruna, firistoci, za su yayyafa jinin a kewaye da bagaden.


Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadayarsa, ya yanka a bakin ƙofar alfarwa ta sujada. 'Ya'yan Haruna maza kuwa, firistoci, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi.


su da suke zaɓaɓɓu bisa ga rigyasanin Allah Uba, waɗanda Ruhu kuma ya tsarkake, domin su yi wa Yesu Almasihu biyayya, su kuma tsarkaka da jininsa. Alheri da salama su yawaita a gare ku.


Kun iso wurin Yesu, matsakancin sabon alkawari, da kuma wurin jinin nan na tsarkakewa, wanda yake yin mafificiyar magana fiye da na Habila.


Sai suka yanka ragon Idin Ƙetarewar. Sa'an nan firistoci suka karɓi jinin daga gare su, suka yayyafa, Lawiyawa kuma suka yi ta fiɗa.


Zai ɗibiya hannunsa a bisa kanta, ya yanka ta a gaban alfarwa ta sujada. 'Ya'yan Haruna, maza, za su yayyafa wa bagaden jinin kewaye da shi.


Sa'an nan ka yanka ragon, ka ɗibi jininsa, ka yayyafa shi kewaye a kan bagaden.


Har wa yau kuma, kowane firist yakan tsaya a kan hidimarsa kowace rana, yana miƙa hadaya iri ɗaya a kai a kai, waɗanda har abada ba za su iya ɗauke zunubai ba.


Da me zan zo gaban Ubangiji, In sunkuyar da kaina a gaban Allah na Sama? Ko in zo gabansa da maraƙi bana ɗaya domin yin hadaya ta ƙonawa?


Zan yayyafa muku tsabtataccen ruwa, za ku kuwa tsarkaka daga dukan ƙazantarku, da kuma daga dukan gumakanku.


Amma yanzu al'ummai da yawa za su yi mamaki a kansa, Sarakuna kuwa za su riƙe baki saboda mamaki. Za su gani su kuma fahimci abin da ba su taɓa sani ba.”


Haihuwar fari ta saniya, ko ta tunkiya, ko ta akuya, ba za ka fanshe su ba, gama su halal ne. Sai kayayyafa jininsu a kan bagade, kitsensu kuma ka ƙone a kan bagaden ƙona hadayu, zai zama turare mai ƙanshi, mai daɗi ga Ubangiji.


Sai kuma ya yanka bunsuru na yin hadaya don zunubin jama'ar ya shigar da jinin bayan labulen. Zai sa jinin kamar yadda ya yi da jinin bijimin, ya yayyafa shi a kan murfin, da gaban murfin.


Firist ɗin zai kawo tsuntsun a bagaden, ya murɗe wuyan tsuntsun, sa'an nan ya ƙone kan a bisa bagaden. Za a tsiyaye jini a gefen bagaden.


Za ka yanka bijimin a gaban Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada.


Zai ɗibiya hannunsa a kan kan hadaya don zunubi, ya yanka hadayar a wurin hadaya ta ƙonawa.


Zai ɗibiya hannunsa a kan kan abin yin hadaya don zunubin, sa'an nan ya yanka a wurin da akan yanka hadaya ta ƙonawa.


Gama ran nama yana cikin jinin, Ubangiji kuwa ya ba su shi a bisa bagade domin a yi wa rayukansu kafara, gama da jini ake kafara saboda akwai rai a cikinsa.


Sai suka yanka bijimin, suka kuma kai yaron wurin Eli.


Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ni Ubangiji Allah, na ce waɗannan su ne ka'idodin bagaden. A ranar da za a kafa shi don miƙa hadayun ƙonawa da yayyafa jini a kansa,


Ka ajiye bagade na yin hadaya ta ƙonawa a gaban ƙofar alfarwa ta sujada,


Zai kuma ɗiba daga cikin jinin, ya sa a bisa zankayen bagaden ƙona turaren da suke cikin alfarwar a gaban Ubangiji. Sauran jinin bijimin kuwa zai zuba shi a gindin bagaden ƙona hadaya wanda yake a ƙofar alfarwa ta sujada.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ