Filibbiyawa 4:8 - Littafi Mai Tsarki8 Daga ƙarshe kuma, 'yan'uwa, ko mene ne yake na gaskiya, ko mene ne abin girmamawa, ko mene ne daidai, ko mene ne tsattsarka, ko mene ne abin ƙauna, ko mene ne daɗɗaɗar magana, in ma da wani abu mafifici, ko abin da ya cancanci yabo, a kan waɗannan abubuwa za ku yi tunani. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20208 A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |